Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiHare-haren ta'addanci na raguwa a jihar Katsina zamanin mulkin Tinubu - Wazirin...

Hare-haren ta’addanci na raguwa a jihar Katsina zamanin mulkin Tinubu – Wazirin Katsina, Ibrahim Ida

Wazirin Katsina, Ibrahim Idah, ya bayyana cewa hare-haren ‘yan ta’adda sun ragu matuƙa a ƙarƙashin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman a jihar Katsina.

Da yake jawabi a taron haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da shugabannin Arewa, Idah ya ce Tinubu ya cika alkawarin yaƙi da bazuwar makamai, wanda hakan ke haifar da raguwar hare-hare idan aka kwatanta da shekarun baya kamar yadda jaridar Premium Times ta sanar.

Ya kuma buƙaci a karfafi rundunar tsaron sa-kai da makamai masu ƙarfi domin ƙarfafa tsaro, sai dai shugaban NDLEA, Buba Marwa, ya ja kunne kan haɗarin hakan, yana mai ba da misalin wani kwamandan sa-kai a Borno da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi tare da zuwa ofishin hukumar da mayaka fiye da 50.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata