Monday, April 6, 2026
HomeWasanniHarin da magoya bayan Kano Pillars suka kai ma 3SC abin Allah-wadai...

Harin da magoya bayan Kano Pillars suka kai ma 3SC abin Allah-wadai ne – Shehu Sani

Tsohon Sanata a Nijeriya, Shehu Sani, ya yi Allah-wadai da rikicin da magoya bayan Kano Pillars suka tafka bayan wasan NPFL da Shooting Stars ta Ibadan a Kano, inda suka kai wa ‘yan wasa da alkalan wasa hari.

Lamarin ya faru ne bayan Shooting Stars ta zura kwallo a minti na 94, inda ya daidaita sakamakon wasan da ya kare 1–1.

Shehu Sani ya bayyana cewa harin abin kunya ne da ke nuna rashin tsaro da kuma sakaci wajen kula da magoya baya a filayen wasa, yana mai cewa hakan na hana jama’a zuwa kallon wasannin cikin gida.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa jami’an tsaro sun yi amfani da barkonon-tsohuwa wajen tarwatsa magoya bayan da suka mamaye fili bayan kammala wasan.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata