Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiHisbah ta ceto kananan yara mata 16 da aka yi safararsu a...

Hisbah ta ceto kananan yara mata 16 da aka yi safararsu a Kano

 

Jami’an hukumar Hisbah a jihar Kano sun yi nasarar kubutar da wasu kananan ‘yan mata su 16 da aka yi safararsu a wata tashar mota a jihar.

Wadanda lamarin ya rutsa da su, dukkansu ‘yan mata ne masu karancin shekaru, an ceto su ne a tashar mota ta Unguwa Uku.

Da yake jawabi mataimakin kwamandan Hisbah, Mujahid Aminuddeen Abubakar ya bayyana cewa jami’ansu sun yi nasarar ceto wasu mutane tare da ceto kananan yaran mata da ake shirin safarar su zuwa Legas da Jamhuriyar Benin da kuma Ghana.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata