Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiHukumar DSS ta maka Sowore, kamfanin Meta da manhajar X kotu

Hukumar DSS ta maka Sowore, kamfanin Meta da manhajar X kotu

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta maka dan gwagwarmaya Omoyole Sowore, kamfanin Meta da kuma manhajar X kotu, sakamakon kalaman sukar gwamnatin Tinubu da Sowore ya wallafa.

Hukumar ta shigar da karar ne a gaban wata kotun tarayya da ke Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wannan ya biyo bayan da hukumar DSS din ta bukaci a dakatar da shafin na Sowore a baya, tare da ba shi wa’adin goge wallafar da ya yi.

Sai dai a martaninsa, Sowore ya sha alwashin halartar kotun kan karar da hukumar ta shigar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata