Hukumar EFCCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, ta ce ta kwato wasu kudade daga kamfanin zuba jarin bogi na CBEX.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda dubban ‘yan Najeriya da suka saka hannun jari a dandalin suka yi asarar kimanin Naira tiriliyan 1.3.
CBEX dai ya rika bai wa masu saka hannun jarin ribar kashi 100 cikin 100 a cikin kwanaki 30, kafin daga bisani ya gudu da kudaden mutanen.
Da yake magana a gidan Talabijin na TVC, shugaban hukumar EFCC Ola Olukoyede, ya cewa hukumar ta EFCC ta kama wasu da ake zargin suna damfarar CBEX, yana mai cewa hukumar na ci gaba da bin diddigin wasu da suka gudu.
