Hukumar EFCC ta bukaci ’yan Nijeriya da su daina yabawa ko girmama mutanen da aka samu da laifin cin hanci da rashawa, tana mai cewa hakan na raunana yaki da almundahana a kasar.
Shugaban sashen shari’a na EFCC reshen Kaduna, Nasir Salele, ya ce abin takaici ne yadda al’umma ke kare wadanda aka yanke wa hukunci, har ma a wasu lokuta su tarbe su da shagali ko ba su sarautar gargajiya bayan fitowa daga gidan yari.
EFCC ta jaddada cewa yaki da cin hanci ba aikin hukuma kadai ba ne, tana kuma kira ga kafafen yada labarai da jama’a su taimaka wajen wayar da kan al’umma da kin amincewa da cin hanci da rashawa.
