Sunday, April 5, 2026
HomeKetareHukumar FCCPC ta ce barazanar Meta na ficewa daga Najeriya ba zai...

Hukumar FCCPC ta ce barazanar Meta na ficewa daga Najeriya ba zai hanata zartar da hukuncin ba- Channels TV

Hukumar kare hakkin mai Saye da Ingancin fasaha (FCCPC) ta bayyana cewa barazanar kamfanin Meta na ficewa daga Najeriya ba ta hana su bin doka ko janye hukuncin da aka yanke masa ba.

A sanarwa da darektan hulda da jama’a na hukumar, Mista Ondaje Ijagwu, ya fitar a ranar Asabar, hukumar ta zargi~ Meta – wadda ke da mallakar WhatsApp, Facebook da Instagram – da kokarin neman tausayin jama’a da neman rage matsin lambar hukuncin da ake nufin dauka a kansa.

Tun a ranar 19 ga Yuli, 2024, FCCPC ta ci tarar Meta dalar Amurka miliyan 220 bisa take hakkin masu amfani da bayanansu na sirri, tare da karya dokar Federal Competition and Consumer Protection Act (FCCPA) da kuma Nigeria Data Protection Regulation (NDPR).

Rahoton binciken ya tabbatar da cewa Meta da WhatsApp – wadanda aka kira da “Meta Parties” – sun aikata abubuwa da dama da suka sabawa doka. Wadannan suka hada da: hukuncin kotun kare hakkin fasaha da ta ci tarar kamfanin $220m da FCCPC ta kakabawa Meta.

A cewar FCCPC, Meta ta taba fuskantar irin wannan hukunci a wasu kasashen duniya kamar Amurka ($1.5bn a Texas), Tarayyar Turai ($1.3bn), da kuma kasashe kamar India, Faransa, Koriya ta Kudu da Ostiraliya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata