Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiHukumar ICPC mai yaki da cin hanci a Nijeriya ta ce ta...

Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci a Nijeriya ta ce ta kwato sama da naira biliyan 20 a shekarar 2024

Shugaban hukumar ICPC, mai yaki da cin hanci a Nijeriya Dr Musa Aliyu ya ce hukumar ta kwato sama da Naira biliyan 20 da wasu kadarori daga hannun wadanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa a shekarar 2024.

Aliyu ya bayyana haka ne a ranar Litinin dinnan a birnin Ilorin yayin da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN a wurin taron manyan lauyoyin gwamnati a shiyyar Arewa ta tsakiya.

Taron an yi shi ne don inganta dabarun yaki da cin hanci da rashawa a kasa a shiyyar Arewa ta tsakiyar Najeriya.

Aliyu ya bayyana cewa cin hanci da rashawa ba a matakin tarayya kadai ba ne, har ma a kananan hukumomi, don haka dole sai an maganceshi ta hanyar fitowa da sabbin dabaru.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata