Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiHukumar "Road Safety“ ta dalilin bukatar bai wa jami‘anta makamai

Hukumar “Road Safety“ ta dalilin bukatar bai wa jami‘anta makamai

Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta “Road Safety” a Najeriya ta bayyana cewa yawan rasa rayuka da jami’anta ke yi ya sa ta neman damar a basu ikon rike makamai a bakin aiki.

Yayin da yake tattaunawa da Premium Times, shugaban hukumar ta kasa Shehu Muhammed ya ce tun bayan kafa hukumar, a kalla jami’ai sama da 200 ne suka rasa rayukansu sakamakon buge su da gangan da masu ababen hawa ke yi.

Ya kara da cewa abin takaici ne yadda ake gaza hukunta wadanda suke aikata irin wannan laifi.

A yanzu haka dai akwai kuduri a gaban majalisun tarayyar Najeriya, wanda ke bukatar a yi kwaskwarima ga dokar hukumar ta shekarar 2007, tare da sahalewa jami’anta rike makami a bakin aiki.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata