Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiHukumar NAPTIP ta kubutar da 'yan Nijeriya 20 da aka yi safarar...

Hukumar NAPTIP ta kubutar da ‘yan Nijeriya 20 da aka yi safarar su

Hukumar yaki da safarar mutane ta Nijeriya NAPTIP, haɗin guiwa da hukumar tsaro ta DIA, sun kubutar da mutane 20 daga gungun masu safarar mutane da ke aiki a ƙasashen Equatorial Guinea da Togo da kuma Najeriya.

Jami’an NAPTIP sun bayyana cewa waɗanda aka ceto an yaudare su da alkawarin samar musu ayyuka masu albashi mai tsoka, sai dai daga bisani aka tilasta musu yin aikin karfi.

Jami’in hulɗa da jama’a na NAPTIP, Vincent Adekoye, ya ce an kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a safarar a Abuja, Osun da Nasarawa, yayin da hukumar ta ƙara sa ido a kan iyakokin ƙasa don hana safarar mutane.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata