Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiHukumar NDLEA ta cafke limamin wata coci a Legas bisa zargin safarar...

Hukumar NDLEA ta cafke limamin wata coci a Legas bisa zargin safarar kwaya daga Ghana

Hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Nijeriya ta kama shugaban cocin The Turn of Mercy, Adefolusho Olasele, wanda aka fi sani da Abbas Ajakaiye, bisa zargin safarar miyagun kwayoyi daga Ghana zuwa Najeriya.

An cafke shi ne a ranar Lahadi, 3 ga Agusta 2025, a cocinsa da ke Okun Ajah, Lekki, bayan jami’an NDLEA sun jira ya gama jagorantar ibada.

Olasele, wanda ya tsere zuwa Ghana a watan Yuni don gudun kamen, ana zarginsa da hannu a haramtattun kaya guda biyu da suka hada da kilo 200 na Ghana Loud da aka kama a Okun Ajah Beach a ranar 4 ga watan Yuni, da kilo 700 da aka samo a motar sa a ranar 6 ga watan Yuli.

Ya amsa cewa ya shigo da kayan ta hanyar ruwa daga Ghana kafin a kama shi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata