Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiHukumar NEMA ta karbi 'yan Nijeriya 147 da suka makale a Libya

Hukumar NEMA ta karbi ‘yan Nijeriya 147 da suka makale a Libya

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA ta bayyana karbar ‘yan kasar 147 da suka makale a Libya.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X, ta bayyana cewa dawo da ‘yan kasar wani bangare ne na shirin mayar da mutane ainahin kasashensu, na hadin gwiwa tsakanin majalisar dinkin duniya da kuma gwamnati.

Labari mai alaka: Hukumomi a Nijeriya sun karbi ‘yan kasar 139 daga jamhuriyar Nijar

Mutanen da hukumar ta karba sun hadar da manyan maza da mata guda 100, sai yara maza da mata 34, sannan jarirai guda 13.

Tuni dai NEMA ta bayyana cewa an fara shirin daukar bayanan su ta hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya, kafin mayar da su cikin al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata