Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiHukumar 'Road Safety' ta kama ababen hawa 250 kan daukar kaya fiye...

Hukumar ‘Road Safety’ ta kama ababen hawa 250 kan daukar kaya fiye da kima a Abuja

Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta Najeriya ta ce ta kama ababen hawa 250 cikin kwanaki biyu kacal, sakamakon samun su da laifin daukar kaya fiye da kima a Abuja.

Kwamandan hukumar reshen Abuja Felix Theman ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da aka fitar, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Sanarwar ta ce wannan mataki na cikin yunkurin hukumar na tabbatar da tsaron lafiyar masu ababen hawa ta hanyar bin doka.

Ta kuma kara da jaddada haramcin daukar fasinjoji biyu a kujerar gaba da wasu direbobin tasi ke yi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata