Hukumar shari’a ta jihar Kano (JSC) ta sauke Adamu Salisu, rijistara a babbar kotu mai lamba 13, daga matakin aiki na Grade Level 13 zuwa na 12 bayan an same shi da laifin ƙirƙirar takardu da sa hannun jabu a matsayin shugaban hukumar shari’a.
Mai magana da yawun hukumar shari’a, Baba Jibo-Ibrahim, ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar bayan taron hukumar karo na 84 da aka gudanar a ranar Juma’a.
An kuma gargade shi da karfin hali da kada ya sake aikata irin wannan ko ya ƙarfafa wasu da yin haka, in ba haka ba za a ɗauki matakin shari’a a kansa.
Haka zalika, an binciki Yusuf Ayuba, mai koyon aiki da ke aiki a babbar kotu ta 8, da ke Miller Road, inda aka same shi da laifin barin aiki na tsawon wata huɗu ba tare da izini ko dalili ba.
Rahoton jaridar Daily Nigerian ya ruwaito hukumar ta ce matakin ya na cikin kokarinta na tabbatar da tsafta, gaskiya da ladabi a bangaren shari’a.
