Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiHukumar SON ta kama tayoyi da wayoyin lantarki na jabu a Nijeriya

Hukumar SON ta kama tayoyi da wayoyin lantarki na jabu a Nijeriya

Hukumar SON mai kula da ingancin kaya a Nijeriya ta ja hankalin cewa akwai tayoyi da wayoyin lantarki marasa inganci da ke yawo cikin kasar.

Babban daraktan hukumar Dr Ifeanyi Chukwunonso Okeke ne ya bayyana damuwarsa da wannan lamari a lokacin da ya jagoranci lalata wasu tayoyi da wayoyin lantarki da wasu kayayyaki marasa inganci da kimarsu ta kai ta bilyoyin Naira a jihar Legas, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Ya koka kan yadda ake samun karuwar kaya marasa inganci da kuma na jabu a manyan kasuwannin da ke fadin kasar, tare da zargin wasu da ya kira masu zagon kasa ga tattalin arzikin kasa da daukar alhakin shigo da su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata