Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta dakatar da dukkan tallace-tallacen magungunan gargajiya da ake nunawa a fina-finan Hausa da na masu shela da makirufo a tituna, saboda karya ƙa’idojin tacewa.
Sakataren Hukumar, Abba El-Mustapha, ya ce yawancin tallace-tallacen ba su wuce tantancewa ba. Inda ya umurci masu tallace-tallacen da su dakatar da duk wata talla a Talabijin ko yanar gizo har sai sun samu lasisi.
An kuma ba su wa’adin mako guda daga 21 ga Mayu, 2025, su mika tallolinsu domin tantancewa ko su fuskanci hukunci.
Hukumar ta roƙi NBC da tashoshin Talabijin su tallafa wajen tabbatar da bin doka da ɗabi’a a cikin al’umma.
