Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiHukumar zabe ta kasa INEC ta sanya ranar gudanar da zabukan gwamna...

Hukumar zabe ta kasa INEC ta sanya ranar gudanar da zabukan gwamna a jihohin Ekiti da Osun 

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, yayin rantsar da sabbin kwamishinonin zabe guda shida da majalisar dokoki ta kasa ta amince da su kwanan nan.

A cewarsa, za a gudanar da zaben gwamna a jihar Ekiti a ranar Asabar, 20 ga Yuni, 2026. Za a fara zaben fidda gwanin ‘yan takara na jam’iyyun siyasa daga ranar 20 ga Oktoba, 2025, sannan a kammala ranar 10 ga Nuwamba, 2025.

Hakanan, jam’iyyu za su rufe shigar da fom din ‘yan takara da yammacin ranar 22 ga Disamba, 2025.

A jihar Osun kuwa, za a gudanar da zaben gwamna a ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata