Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiHukumar Zaben Nijeriya na son ayi dokar da za ta hana zuwa...

Hukumar Zaben Nijeriya na son ayi dokar da za ta hana zuwa da sama da naira dubu 50 a rumfar zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta a Nijeriya INEC ta bukaci majalisa ta yi dokar haramta zuwa da kudade masu yawa a rumfunan zabe domin magance matsalar sayen kuri’a da kuma magudin zabe.
Daraktan sashen dokoki na hukumar Tanimu Muhammed, SAN, ne ya yi wannan kiran a yayin wani taron kan sake gyaran dokokin zabe da kwamitin majalisar wakilai kan zabe ya shirya a Abuja.
Tanimu Muhammed ya bukaci ‘yan majalisa da su fito da dokar da zata saka naira dubu hamsin a matsayin mafi karancin kudin da mutum zai iya rika wa a kusa da rumfunan zabe.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata