Sunday, April 5, 2026
HomeKetareHukumomin mulkin sojan Nijar sun kama wasu 'yan jarida uku na Radio...

Hukumomin mulkin sojan Nijar sun kama wasu ‘yan jarida uku na Radio Sahara da ke jihar Agadez

Rahotanni daga gidan Radio Sahara Fm da ke jihar Agadez sun tabbatar da kama wasu ‘yan jaridar gidan radiyon guda uku da suka hada da Hamid Mahmoud tsohon wakilin Muryar Amurka (VOA), da Maman Bachir Sani da kuma Masaouda Jaharou Sanda

Malan Anisse daya daya daga cikin shugabannin kafar ya shaida wa DCL cewa tun ranar Alhamis ne aka kama abokan aikin nasu, kuma har yanzu haka ana cigaba da tsare su a ofishin hukumar ‘yan sanda na jihar kafin a gabatar da su a gaban alkali.

An kama wadannan ‘yan jaridar ne dai sakamakon zargin su da bada labarin da ba gaskiya ba, kan cewa hukumomin kasar Nijar sun yanke hulda da hukumomin Rasha da na Turkiyya wanda suka ce su ma sun same shi ne daga wata kafa ta ketare.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata