Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiIHR ta jinjina wa NAHCON da sauran masu ruwa da tsaki kan...

IHR ta jinjina wa NAHCON da sauran masu ruwa da tsaki kan yadda jigilar mahajjatan Nijeriya ke gudana

Kungiyar nan da ke yada ayyukan da suka jibinci hajji wato Independent Hajj Reporters IHR, ta yaba wa shugabancin Hukumar Hajji ta Kasa NAHCON, kamfanonin jiragen sama da ke jigilar alhazai, da masu yin hidima a Saudiyya har da alhazan kansu saboda yadda aka gudanar da shirye-shiryen Hajjin 2025 daga Nijeriya cikin nasara har zuwa yanzu.

Kungiyar ta bayyana cewa hukumar NAHCON ta gudanar da jigilar alhazai fiye da 21,075 zuwa Saudiyya ba tare da wata babbar matsala ba.

A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa, Ibrahim Muhammed, ya rattaba wa hannu, IHR ta ce, “Bayanan da muke da su sun nuna cewa kusan duk masu ruwa da tsaki a jigilar alhazai da karbarsu suna bakin kokarinsu, shi ya sa aka samu irin wannan nasara.”

Duk da haka, kungiyar ta bukaci a ci gaba da wannan irin himma yayin da alhazai ke ci gaba da tafiya daga Madina zuwa Makka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata