Babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya PDP ta yi alwashin cewa hukumar zabe ta kasa INEC ba ta isa ta dakatar da taron ta na NEC da za ta yi ranar 30 ga wannan wata na Yuni ba.
Da yake magana a taron manema labarai a Abuja sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Hwanarabul Debo Ologunagba ya ce shirye-shiryen taron sun yi nisa.
A kwanakin baya ne dai INEC ta rubutawa jam’iyyar PDP wasika ta na korafin cewa sanarwar da ta aike mata na taron NEC ba tayi dai dai ba, saboda ba shugaban jam’iyyar na kasa da sakataren jam’iyyar ba su sanya hannu a takardar ba.
Sai dai Debo Ologunagba ya yi zargin cewa mukaddashin sakataren hukumar ta INEC, Halilu Aminu, wanda ya sanya hannu kan wasikar, yana kokarin taimakawa jam’iyyar APC ne kawai don ci gaba da gudanar da ayyukanta.
