Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaINEC na duba buƙatun kungiyoyi 110 da ke neman rigista a matsayin...

INEC na duba buƙatun kungiyoyi 110 da ke neman rigista a matsayin jam’iyyun siyasa a Najeriya

Hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana cewa ta karɓi wasikun buƙatun rajistar sabbin jam’iyyu 110 daga kungiyoyi daban-daban har zuwa Litinin, 23 ga watan Yunin, 2025.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce ana ci gaba da duba buƙatun bisa doka da tsarin da aka shimfiɗa inda ya ce sun riga sun amsa duk buƙatun da aka aika, banda guda shida da za a amsa kafin ƙarshen mako.

Hukumar ta INEC ta fitar da cikakken bayanan jerin sunayen kungiyoyin da ke neman rajista da sunayensu, takaitattun haruffansu, adireshisu, da shugabanninsu a jumlace.

Kuma hukumar cikin sakon da ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce za a wallafa jerin gwanon su a shafin yanar gizo da kafafen sada zumunta na hukumar don samun gamsashshiyar fahimta kan kudirin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata