Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta gabatar da buƙatar kasafin kuɗi na Naira biliyan 873.78 domin gudanar da babban zaɓen shekarar 2027.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya gabatar da wannan buƙata ne a gaban kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dattawa da ta Wakilai kan Harkokin Zaɓe a Majalisar Ƙasa, a ranar Alhamis.
Ya bayyana cewa tuni aka fara shirye-shiryen zaɓen 2027 bisa tanadin doka da ke buƙatar a amince da kuɗaɗen zaɓe aƙalla kwanaki 360 kafin ranar da za a gudanar da zaɓen.
Taron kare kasafin kuɗin ya samu jagorancin Sanata Simon Bako Lalong, tare da takwaransa daga Majalisar Wakilai, Hon. Adebayo Balogun.
