Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiINEC ta ja kunnen jam'iyyun siyasa a Nijeriya game da fara yakin...

INEC ta ja kunnen jam’iyyun siyasa a Nijeriya game da fara yakin neman zabe da wuri

Hukumar zaben Nijeriya INEC ta gargadi jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su guji fara yakin neman zabe gabanin zabukan 2027, inda ta bayyana hakan a matsayin karya dokar zabe.

Gargadin na INEC ya zo ne a daidai lokacin da ake samun yawaitar tarukan siyasa a fadin kasar, da sanya allunan hotunan ‘yan takara a allunan talla.

Sakataren yada labaran shugaban hukumar ta INEC, Rotimi Oyekanmi, ya ce har yanzu hukumar ba ta fitar da jadawalin zaben 2027 ba.

Kazalika ba a gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyu ba, kuma babu wata jam’iyyar siyasa da ta fitar da sunayen ‘yan takara a babban zaben mai zuwa ba,yin hakan ya sabawa sashi na 94,(1) na dokar zabe ta 2022.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata