Iyalan tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai sun bayyana damuwarsu kan ci gaba da tsare shi ba bisa ka’ida ba a hannun Hukumar ICPC, duk da cewa umurnin kotun magistare da aka samu don tsare shi ya ƙare.
A wata sanarwa da dan sa, Mohammed Bello El-Rufai, ya sanyawa hannu a madadin ƴan uwansa, sun ce an kama El-Rufai ne tun 18 ga Fabrairu 2026, sannan ICPC ta samu umarnin kotun majistare na tsare shi ranar 19 ga Fabrairu, amma umarnin ya ba da damar tsare shi na kwanaki 14 kacal.
Iyalan sun bayyana cewa wa’adin kwanakin ya riga ya cika, amma har yanzu ba a gurfanar da shi a kotun da ta dace ba, kuma ba a sake samun wani sabon izini daga kotu da zai ba da damar ci gaba da tsare shi ba.
