Hukumar JAMB ta bayyana Asabar, 28 ga watan Yunin, 2025 a matsayin ranar da za a gudanar da jarrabawar mop-up ta UTME na bana.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Dr. Fabian Benjamin ya fitar, JAMB ta ce ɗalibai 96,838 ne za su rubuta wannan jarrabawa, ciki har da 5,096 da suka fuskanci matsalar tantance bayanan yatsa da kuma 91,742 da ba su halarci jarrabawar baya ba.
Hukumar ta bukaci waɗanda abin ya shafa su fara cire takardun shaidar jarrabawar daga ranar Litinin, 23 ga watan Yuni.
Za a gudanar da jarrabawar a cibiyoyi 183 a faɗin ƙasa, Yayin da hukumar ta sanar da cire cibiyoyi 113 da aka samu da laifin rashin inganci da maguɗi kamar yadda rahoton jaridar Punch ya tabbatar.
