Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiJami’an ’yansanda akalla 150 za su fuskanci kwamitin ladabtarwa

Jami’an ’yansanda akalla 150 za su fuskanci kwamitin ladabtarwa

Akalla manyan jami’an ’yansanda 150 ne ke fuskantar kwamitin ladabtarwa a sassa daban-daban na rundunonin ‘yansandan sakamakon aikata wasu laifuffuka.

An bayyana cewa, jami’an ‘yansandan masu mukamin ASP zuwa sama za su fuskanci kwamitin ladabtarwa bisa laifukan da suka shafi karya dokokin aiki da kwarewa.

Jaridar DailyTrust ta ruwaito cewa, ana sa ran kwamitin da ya fara zama a ranar Litinin 14 ga watan Yuli zai kammala bincike a kwana 10 tare da isar da sakamakon binciken ga hukumar ‘yansanda ta kasa inda su kuma su aiwatar da hukuncin ga jami’an da ake tuhuma.

Binciken ya biyo bayan korafe-korafe daga daidaikun mutane da kuma kungiyoyi ga shugaban ‘yansandan Nijeriya, Koyode Egbetokun kan ayyukan jami’an na musguna ma jama’a da kuma tatsar kudadensu ba bisa ka’ida ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata