Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaJam’iyyar ADC ta sanar da kwana uku na alhinin rashin tsohon Shugaban...

Jam’iyyar ADC ta sanar da kwana uku na alhinin rashin tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari

Jam’iyyar ADC ta bayyana kwanaki uku na zaman makoki ga mambobinta don girmama marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi a birnin Landan.

Sanarwar, wacce shugaban jam’iyyar na rikon ƙwarya, Sanata David Mark, ya fitar a Kano, ta bayyana Buhari a matsayin jagora wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa ƙasa – a matsayin soja da kuma shugaban farar hula.

David Mark ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da kammala manyan ayyukan raya ƙasa da Buhari ya fara, domin cigaba da amfani da su ga al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata