Jam’iyyar ADC mai hamayya a Nijeriya, ta soki gwamnatin shugaba Tinubu kan damar da ta bai wa Amurka wajen kaddamar da hari kan ‘yan ta’adda a jihar Sokoto.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta a Nijeriya Bolaji Abdullahi ya fitar a shafinsa na X, ya ce ya zama wajibi Nijeriya ta dauki alkalin kare kanta da kuma samar da tsaro cikin gida ba tare da sa hannu daga waje ba.
Haka kuma, ya ce hakan na nuni da yadda Tinubu wanda ke da alhakin jan ragamar shugabanci ya koma baya, lamarin da ta ce abin tambaya ne, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Jam’iyyar dai, ta ce kamata yayi irin wannan mataki ya zama na karshe da za a iya dauka idan har an rasa duk wata damar kawo karshen matsalar tsaro a Nijeriya.
