Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiJam'iyyar APC ta kalubalanci Gwamnan Filato Mutfwang da ya bayyana masu matsa...

Jam’iyyar APC ta kalubalanci Gwamnan Filato Mutfwang da ya bayyana masu matsa masa lamba ya bar PDP

Jam’iyyar APC ta jihar Filato ta kalubalanci Gwamna Caleb Mutfwang da ya fito fili ya bayyana sunayen mutanen da ke matsa masa lamba ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC.

Gwamnan ya bayyana a wani taro a fadar gwamnati da ke Jos cewa wasu jiga-jigan APC sun roƙe shi da ya shiga jam’iyyarsu, amma ya ce sai idan Allah da kuma jama’ar jihar sun yarda zai iya yanke wannan shawarar.

Sai dai mai magana da yawun jam’iyyar APC na riko a jihar, Shittu Bamaiyi, ya musanta ikirarin gwamnan, yana mai cewa wannan magana tana nuni ne da yadda gwamnatin Mutfwang ta gaza cika alkawuran da ta dauka ga al’umma,inda ya ce idan gaskiyane ya fito ya faɗi sunayen waɗanda ke matsa masa lamba, ya kuma bayyana su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata