Jiga-jigan jam’iyyar PDP daga yankin Arewa maso Yamma sun nesanta kansu daga amincewar da aka yi da tsohon ministan ayyuka na musamman, Tanimu Turaki, SAN, a matsayin dan takarar shugabancin jam’iyyar na kasa daga yankin.
Mai shirya al’amuran jam’iyyar a matakin kasa, Umar Bature, wanda ya yi magana da manema labarai a Abuja daren Alhamis, ya ce amincewar da aka sanar ba ta wakilci matsayar shugabannin yankin baki ɗaya ba.
Bature ya bayyana matakin a matsayin na mutum ɗaya da aka yanke ba tare da cikakkiyar shawarar shugabannin yankin ba, yana mai cewa Arewa maso Yamma ba ta taɓa zama ta yanke hukunci kan wannan matsayi ba, kuma ba ta amince da kowa a matsayin dan takara ba.
Maganarsa ta biyo bayan sanarwar da gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce an amince da Turaki a matsayin dan takarar hadin-kai na Arewa. Sai dai Fintiri ya ƙara da cewa duk wanda bai gamsu da wannan matsaya ba yana da ‘yancin tsayawa takara.
