Jam’iyyar PDP ta bukaci Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya janye jerin sunayen jakadu 32 da ya tura majalisar dattawa, tana mai cewa jerin ya ƙunshi mutane da ake kallon su marasa nagarta a idon ’yan Nijeriya da ma duniya. PDP ta ce wannan abu abin kunya ne ga diflomasiyyar ƙasar.
A cewar mai magana da yawun jam’iyyar, Comrade Ini Ememobong, PDP ta ce akwai sunayen mutane da ake zargi da aikata abubuwan da suka saba wa dimokuraɗiyya, ciki har da tsohon shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.
Jam’iyyar ta yi zargin cewa saka shi a cikin jerin zai iya zama hanyar matsa wa sabon shugaban INEC wajen gudanar da zaɓe cike da kura-kurai kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
PDP ta ce tana bukatar a sake tura sunayen ’yan Nijeriya masu nagarta da tarihin kare dimokuraɗiyya, waɗanda za su wakilci ƙasar da mutunci a kasashen waje.
Jam’iyyar ta ce jinkirin da Shugaba Tinubu ya yi kafin fitar da jerin na nuna ƙarancin mutanen kirki da yake da su a kusa da shi.
