Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiJihohi na taka rawa a yadda Nijeriya ke bai wa ƙasashen waje...

Jihohi na taka rawa a yadda Nijeriya ke bai wa ƙasashen waje wuta duk da ƙarancinta a gida – Hukumar makamashi

Shugaban Hukumar Makamashin Nijeriya (ECN), Mustafa Abdullahi, ya bayyana cewa, duk da ƙarancin wuta a cikin gida, Najeriya na ci gaba da bai wa ƙasashen waje makamashi tare da ƙara ƙoƙari wajen sauyawa zuwa makamashin da ba ya gurbata muhalli.

A hirarsa da Channels Television, Abdullahi ya ce Najeriya na samar da megawatt 6,000 na wuta a yanzu, wanda ya haura sama da megawatt 4,000 da ake da shi kafin shekarar 2023.

Ya bayyana cewa kashi 60% na ‘yan ƙasa na samun wuta, sai dai har yanzu mutane miliyan 85 ba su da damar amfani da ita.

Ya danganta matsalar yawan katsewar wuta da tsoffin layukan isar da lantarki da kuma ƙarancin hanyoyin samarwa.

Abdullahi ya ƙara da cewa sabuwar dokar wutar lantarki ta bai wa jihohi damar samar, rarrabawa da kuma sa ido kan wutar lantarkinsu.

Sai dai, jinkirin aiwatar da wannan tsarin, da ake ganin ya samo asali ne daga ƙarancin ƙwarewa a matakin jihohi, inda ECN ke ci gaba da horar da su domin cike gibin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata