Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiJihohin Arewa 4 ne kawai ke biyan 'yan fansho mafi karancin albashin...

Jihohin Arewa 4 ne kawai ke biyan ‘yan fansho mafi karancin albashin N32,000 – kungiyar ‘yan fansho

Kungiyar ‘yan fansho ta Nijeriya NUP ta ce jihohi hudu ne kacal cikin 19 na jihohin Arewa suka bi umarnin gwamnatin tarayya na biyan ₦32,000 mafi karancin albashi na wata-wata.

Da yake jawabi Yayin taron shiyyar da ya gudana a jihar Kaduna, shugaban NUP, Kwamared Mohammed Sali, ya bayyana lamarin a matsayin Rashin adalci ga tsofaffi da suka sadaukar da shekaru da dama na yi wa kasa hidima.

Ya ce jihohi hudu ne kawai ke biyan mafi karancin ₦32,000 daga cikin 19 a duk wata.

A cewarsa jihohi da dama har Yanzu suna biyan kasa da ₦3,000, ₦4,000, ko ₦5,000,kuma wannan ba daidai ba ne indai ba so ake a gansu akan titi suna yawo ba.

Sakataren kungiyar Alhassan Balarabe Musa, ya kuma yi Allah-wadai da banbance-banbance tsakanin kudaden fansho na ‘yan fansho da wanda ‘yan siyasa ke samu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata