Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiCire tallafin man fetur ya taimaka wa jihohin Nijeriya 27 rage karɓar...

Cire tallafin man fetur ya taimaka wa jihohin Nijeriya 27 rage karɓar bashin cikin gida – Rahoton DMO

Hukumar kula da bashin cikin gida DMO ta bayyana cewa jihohin Nijeriya 27 cikin 36 sun rage karɓar bashin cikin gida a cikin watanni 15 da suka gabata.

Wannan ya biyo bayan ƙarin kuɗaɗen shiga daga asusun tarayya sakamakon cire tallafin fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi.

Yanzu jihohi, tarayya da ƙananan hukumomi suna raba N1.6 tiriliyan a wata, sabanin ƙasa da tiriliyan daya da ake rabawa a baya.

A watan Yuni kadai, rahoton jaridar The Nation ya Ambato yadda aka raba Naira tiriliyan 1.8: inda gwamnatin tarayya ta samu Naira biliyan 645, jihohi suka samu Naira biliyan 607, yayin da ƙananan hukumomi suka kasafta Naira biliyan 444.

Sannan jihohin da ke samar da mai suka samu jumillar kudaden da basu kasa Naira biyan 120 ba, a matsayin kaso na haƙƙinsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata