Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiJihohin Nijeriya sun kashe N455bn don biyan basukan ketare a shekarar 2025...

Jihohin Nijeriya sun kashe N455bn don biyan basukan ketare a shekarar 2025 – NBS

Bayanai daga hukumar kididdiga ta Nijeriya NBS sun nuna cewa jihohin Nijeriya sun kashe N455.38bn wajen biyan basukan ketare a shekarar 2025.

Hakan na nuni da kari da sama da kaso 25 a kudaden da suka kashe a shekarar 2024, inda suka biya N362.08bn, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Masana fannin tattalin arziki dai sun nuna damuwa da cewa hakan na yin barazana ga damar gwamnatocin na gabatar da wasu manyan ayyuka, biyan albashin ma’aikata da kuma gabatar da harkokin yau da kullum.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata