Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiJinkirin gyaran Dokar Zabe na iya shafar jadawalin zaben 2027 — INEC

Jinkirin gyaran Dokar Zabe na iya shafar jadawalin zaben 2027 — INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta ce jinkirin yin gyara ga Dokar Zabe na iya shafar jadawalin gudanar da zaben 2027.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da Kungiyoyin Fararen Hula (CSOs) a ranar Laraba a Abuja.

Ya ce duk da jinkirin amincewa da kudirin gyaran Dokar Zaben da ke gaban Majalisar Tarayya a halin yanzu, hukumar INEC na ci gaba da shirye-shirye domin gudanar da babban zaben 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata