Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiJiragen yakin sojin saman Nijeriya sun yi ajalin mayaka da dama a...

Jiragen yakin sojin saman Nijeriya sun yi ajalin mayaka da dama a hare-haren sama a dutsen Mandara

Rundunar sojin sama ta Najeriya, karkashin Operation Hadin Kai, ta kai gagarumin farmaki na sama kan sansanonin ‘yan
ta’adda a Dutsen Mandara da ke jihar Borno a ranar Lahadi.

Dutsen Mandara na kan iyakar Najeriya da Kamaru, kuma an tabbatar da cewa ya zama mafakar mayakan Boko Haram na bangaren Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad (JAS).

A wata sanarwa da mai magana da yawun NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar a Abuja, wadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito ya ce an kai hare-haren ne bayan bayanan leken asiri sun tabbatar da tarin kayan aiki da zuwan manyan kwamandojin JAS a yankunan Wa Jahode da Loghpere.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata