Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiJita-jitar da ake yadawa a matsayin dalilin rashin halartar taron majalisar koli...

Jita-jitar da ake yadawa a matsayin dalilin rashin halartar taron majalisar koli kanzon-kurege ce – Ministan Abuja

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana dalilin da yasa bai halarci taron majalisar koli ta kasa ba, wanda aka zabi Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban Hukumar INEC.

Wike ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da hanyoyin shiga unguwar Sector Centre B a Dakibiyu, Abuja, a ranar Talata, inda ya ce ya bai wa karamar ministar Abuja, Dr. Mariya Mahmoud damar wakiltarsa a taron saboda wasu ayyuka da ya rigaya ya tsara.

Wike ya musanta rahotannin da ke cewa bai halarci taron ba ne saboda an ki karbar sunan wanda ya nema a ba matsayin shugaban INEC, yana mai cewa labarin na da manufar bata suna da siyasar karya ce.

Ya kuma kara da cewa, ya sanar da Shugaban Kasa tun farko cewa zai tura karamar minista ta wakilce shi saboda wasu ayyuka da ya rigaya ya tsara kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata