Fitaccen gwarzon kokawar “Wrestling”, John Cena, ya yi ritaya bayan wasan bankwana da ya yi a Capital One Arena da ke Washington DC. Cena ya fuskanci Gunther a gasar Saturday Night’s Main Event, inda aka tilasta masa mika wuya bayan rike shi da sleeper hold, lamarin da ya jefa magoya baya cikin alhini.
Wasan ya dauki kusan mintuna 25, kuma shi ne karo na farko da John Cena ya taba mika wuya a tarihin kokawarsa. Bayan kararrawa ta buga, ‘yan kokawa daga dakin ‘yan wasa sun fito domin girmama shi, yayin da Cena ya bar abin hannunsa da takalmansa a cikin zobe, alamar yin ritaya, kafin ya yi bankwana da magoya baya.
John Cena na barin “wrestling” a matsayin gwarzo sau 17 na duniya, wanda shi ne mafi yawa a tarihin wasan. Ya fara kokawa a 2002, ya shahara da taken “You Can’t See Me”, sannan daga baya ya yi fice a fina-finai. Masana da magoya baya na kallonsa a matsayin daya daga cikin mafi girman ‘yan kokawa da WWE ta taba samu.
