Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaKa dawo jam’iyyar PDP, inda aka san darajarka – Kiran Gwamna Bala...

Ka dawo jam’iyyar PDP, inda aka san darajarka – Kiran Gwamna Bala ga Peter Obi

Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, kuma Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya karɓi bakuncin tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, a gidan gwamnatin Bauchi, ranar Juma’a.

Yayin tarbar Obi tare da mambobin *Obidient Movement*, a tattaunawarsa da ’yan jarida, Gwamnan ya bayyana cewa gabanin zaben 2027, dole ne a haɗa kan jam’iyyun adawa. Ya bukaci Peter Obi da ya koma PDP, inda aka san darajarsa tun farko.

Ya ce dole ne a daidaita manufofi da muradu domin amfanin al’ummar Najeriya. A cewarsa, ya kamata jam’iyyun adawa irin su ADC, PDP da sauran su, su haɗu wuri daya domin amfanin jama’a.

A nasa ɓangaren, Peter Obi ya ce ziyararsa Bauchi ta mayar da hankali ne kan tattaunawa da matasa a kwalejojin kiwon lafiya da kuma almajirai.

Da yake magana kan yanayin siyasar Najeriya, Obi ya jaddada cewa dole siyasar ƙasar ta sauya zuwa siyasar ci gaba, cancanta da tausayi, domin tabbatar da cigaba mai ɗorewa.

Ya ce ganawarsa da Gwamna Bala ta shafi tattaunawa kan halin da Najeriya ke ciki, tare da jaddada bukatar haɗin kai don tunkarar zaben 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata