Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaKa fito ka baiwa Tinubu haƙuri kan zargin nuna bambanci a ayyuka...

Ka fito ka baiwa Tinubu haƙuri kan zargin nuna bambanci a ayyuka – Sakon ministan ayyuka ga Kwankwaso

Ministan ayyuka na Nijeriya, David Umahi, ya bukaci tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da ya baiwa Shugaba Bola Ahmed Tinubu haƙuri, bisa zargin da ya yi cewa gwamnatin Tinubu na fifita kudancin Najeriya fiye da arewa wajen rabon ayyukan raya ƙasa.

A wata sanarwa da Umahi ya fitar, wadda mai ba Shugaba Tinubu shawara kan bayanai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya wallafa a dandalin X, ministan ya ce zargin Kwankwaso “ba daidai ba ne rudani ne na siyasa.”

Gidan talabijin na Channels ya Ambato ministan ya ce a gaskiya, Shugaba Tinubu ya fi mai da hankali wajen raya Arewacin Najeriya, musamman Arewa maso Yamma — yankin da Kwankwaso ya fito, fiye da Kudu.

Ya buga misalin manyan ayyukan da ke gudana a Arewacin Najeriya akwai mai tsawon kilomita 1,068 daga Sokoto zuwa Badagry, wanda ya bayyana a matsayin gagarumin aikin da zai haɗa Arewaci da Kudanci da hanya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata