Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaKa fito ka bayyana wa ‘yan Nijeriya hakikanin dalilin da ya sa...

Ka fito ka bayyana wa ‘yan Nijeriya hakikanin dalilin da ya sa ka canza hafsoshin tsaro – Bukatar ADC ga shugaba Tinubu

Jam’iyyar ADC ta bukaci shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya bayyana gaskiya ga ’yan Nijeriya kan ainihin dalilan da suka sa aka yi gaggawar sauya shugabannin rundunonin tsaron Nijeriya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi ya fitar, ADC ta bayyana damuwa kan yadda aka yi wannan canji a daidai lokacin da ake ta rade-radin yunƙurin juyin mulki a ƙasar.

Abdullahi ya ce kodayake Shugaban Ƙasa na da ikon yin irin waɗannan canje-canje, amma abin damuwa ne ganin cewa mafi yawan hafsoshin da aka cire sun shafe watanni 28 kacal a mukamansu, ciki har da shugaban rundunar tsaro wanda aka naɗa a matsayin shugaban sojojin ƙasa shekara ɗaya da ta wuce.

Bolaji ya ƙara da cewa, irin wannan mataki yana da tasiri mai zurfi ga zaman lafiyar rundunonin tsaro, don haka bai kamata a ɗauke shi ba tare da hujja mai ƙarfi ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata