Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiKada ku wargaza Nijeriya, wani dattijo ya ja kunnen Atiku da El-Rufa'i

Kada ku wargaza Nijeriya, wani dattijo ya ja kunnen Atiku da El-Rufa’i

Wani tsohon dan siyasa kuma mai fada a ji, Cif Adesunbo Onitiri, ya ja kunnen tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsoffin gwamnoni Nasir el-Rufai da Peter Obi kan siyasar 2027.

Cif Onitiri ya gargadi wadannan jiga-jigan ‘yan siyasa musamman a kan yin wanu abu ko kalamai da ka iya dagula siyasar Nijeriya a daidai lokacin da al’ummar kasar ke tunkarar babban zaben 2027.

A wata sanarwa da ya fitar a Legas, Onitiri ya bukaci mutanen uku wadanda ya amince da su a matsayin manyan jigogin siyasar Nijeriya kuma masu fada a ji da su nuna matukar kamun kai da kishin kasa a harkokinsu na siyasa.

Ya nanata cewa karuwar tashe-tashen hankula na siyasa na haifar da babbar barazana ga dorewar dimokradiyyar kasar.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata