Shugaban kwamitin WHO, Vivek Murthy ya bayyana cewa binciken hukumar ya gano aƙalla mutane 871,000 ne ke mutuwa a duniya duk shekara sakamakon kadaici.
A cewar WHO, ɗaya cikin shida na al’ummar Duniya na fama da kadaici, wanda ke haddasa cututtuka irin su bugun zuciya, ciwon sukari, hawan jini, damuwa, firgici, har ma da yi wa kai lahani.
Ta ce matasa masu kadaici na da yiyuwar samun ƙasa da kashi 22% na sakamako fiye da takwarorinsu, yayin da manya ke fuskantar matsala wajen samun ko riƙe aiki.
Rahoton wadda jaridar Punch ta ambato WHO na bayyana cewa kadaici na da tasiri ga lafiyar jama’a da tattalin arziki, inda aka kiyasta asarar biliyoyin kuɗi ta fannin lafiya da aikin yi.
