Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaKafin goma na safe na kayar da Matawalle idan ya sake tsayawa...

Kafin goma na safe na kayar da Matawalle idan ya sake tsayawa takarar gwamna a 2027 – Gwamna Dauda Lawan

A wata hira da gidan talabijin na Channels, an jiyo Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfa na cewa kiran da APC da wasu ke yi masa tamkar karkatar da hankali ne, domin a zaben 2023 ma duka manyan jiga-jigan APC sun hada kai amma bai hana shi samun nasara ba.

Rahoton Jaridar Daily Trsut ya Ambato gwamnan na cewa “Ina addu’ar Allah ya sa Matawalle ya sake tsayawa takara a 2027. Kafin karfe 10 na safe, insha Allah, zan gama da shi,”.

Ya ce bai jin tsoron kowane dan takara, domin iko daga Allah ne, kuma har yanzu ba a ga wani sauyi daga wajen Matawalle da zai ba shi rinjaye.

Kan rikicin cikin gida da sauya sheka zuwa ADC, Lawal ya ce babu wata jam’iyya a Najeriya da ba ta da matsala.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata