Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiKamfanin Dangote Cement ya sake bai wa direbobinsa horo kan tuki a...

Kamfanin Dangote Cement ya sake bai wa direbobinsa horo kan tuki a Nijeriya

Kamfanin siminti na Dangote Cement ya ƙara azama wajen horar da direbobinsa domin inganta tsaro a hanyoyin mota tare da rage aukuwar haɗurra a fadin ƙasar.

A lokacin taron shekara-shekara na direbobi da aka gudanar a Ibese, Jihar Ogun, Daraktan kamfanin, Arvind Pathak, ya bayyana cewa horon ya yi daidai da manufar kamfanin ta Absolute Safer Road Policy.

Rahoton jaridar The Guardian ya ce fiye da direbobi 900 ne suka halartar, kuma wani babban taron horo na gaba zai gudana a Obajana, Jihar Kogi.

A cikin watanni biyu kacal, fiye da direbobi 2,000 ne suka kamala wannan tsari, sai dai kawai waɗanda suka cika ƙa’idodi ake ba lasisin tuka motocin kamfanin, in ji shi.

Ya ƙara da cewa kamfanin na haɗa kai da hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da bin ƙa’idoji da kuma hukunta direbobin da suka saba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata