Sunday, April 5, 2026
HomeNishadiKamfanin Meta ya goge shafukan bogi fiye da miliyan 10 a Facebook...

Kamfanin Meta ya goge shafukan bogi fiye da miliyan 10 a Facebook a tsakiyar 2025

Kamfanin Meta da ke da mallakin shafin sada zumunta na facebook ya bayyana gyara a shafin, inda ya sanar da cire shafuka Miliyan 10 na bogi da kuma na damfara 500,000 a farkon rabin shekarar 2025.

Meta ya sanar da yin hakan a matsayin wani mataki domin dakile masu shafukan sojan gona, kwaikwayo da kuma mu’amalar bogi don inganta asalin masu aiki da kuma yada su.

Kamfanin ya kuma kara da cewa, matakin ya shafi masu dauko ayyukan wasu ba tare da izini ba ko kuma sauya-sauye a cikinsa. Hukuncin ba zai tsaya ga rasa damar samun kudade ba a shafin, har da raguwar masu kallo ko mu’amala da aikin mutum a Facebook.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata