Dandalin sada zumunta na Whatsapp mallakar Meta dai ya ce ya bullo da wannan tsari na aminci don taimakawa masu amfani da shi, da kuma guje wa zamba a cikin daidaikun mutane.
A cewar WhatsApp, sabon tsarin an yi shine domin bai wa masu amfani da shi ƙarin tsaro, musamman lokacin da aka saka su cikin rukuni ko fara tattaunawa da mutanen da ba sa cikin abokan hulɗarsu wato Groups.
Kamfanin ya ce a cikin watanni shida na farkon wannan shekara, a wani bangare na aikinsu na ci gaba da kare mutane daga zamba, WhatsApp ya gano tare da rufe manhajar fiye da mutane miliyan 6.8 da ke da alaka da cibiyoyin zamba.
