Thursday, April 9, 2026
HomeLabaraiKananan hukumomi bakwai a Kwara sun rufe kasuwannin shanu

Kananan hukumomi bakwai a Kwara sun rufe kasuwannin shanu

Shugabannin ƙananan hukumomi bakwai da ke yankin Kwara ta Kudu sun bayar da umarnin rufe dukkan kasuwannin shanu a yankin sakamakon matsalolin tsaro.

Wannan matakin ya biyo bayan wani taron tsaro da suka gudanar tare da jami’an soji da sauran masu ruwa da tsaki ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025.

Sanarwar ta bayyana cewa matakin rufewar zai fara aiki daga Jumma’a, 19 ga watan Satumba, 2025, kuma za ta ci gaba har sai baba ta gani.

Haka kuma rahoton jaridar Punch ya ce duk sauran kasuwannin kayan gona a yankin za su rufe da misalin 6 na yamma a ranakun kasuwa biyo bayan fama da hare-hare a ‘yan makonnin nan.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata